Ambaliyan Ruwa Ya Yi Barna a Jihar Adamawa

Ambaliyan Ruwa a JIhar Adamawa

Dukiya ta miliyoyin naira da dabbobi ne suka salwanta a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya sakamakon ambaliyan ruwa da aka yi a yankin Shelleng dake kudancin jihar.

Ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a Shelleng cikin karamar hukumar Shelleng a jihar Adamawa ya yi sanadiyar ambaliyan ruwan da ya haddasa dimbin asara

Kawo yanzu jama’a da dama ne suka rasa gidajensu sakamakon wannan ambaliyan ruwan .

Kamar yadda rahotanni ke cewa wannan ambaliya ya biyo bayan ruwan da aka ta tafkawa ne kamar da bakin kwarya,yasa jama’a da dama sun rasa gidajensu koda yake ba a bayyana adadin wadanda lamarin ya shafa ba, ko suka rasa rayukansu.

Wani dan sakai da ya taimaka wajen ceto wadanda lamarin ya shafa ya bayyana cewa baya ga gidaje,suma dabbobi da gonaki basu tsira ba yayin wannan ambaliyar.

Ba tun yau ba ne dai hukumomi a jihar ke gargadi musamman ga wadanda ke zaune a gabar ruwa da su hanzarta kauracewa wuraren ganin cewa masana na harsashen cewa akwai yiwuwar samun munananan ambaliya a bana,batun da gwamnan jihar Adamawan Sen.Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ke cewa dole a fadakar da jama’a.

Jihar Adamawa dai jiha ce dake da manyan koguna da kuma madatsun ruwa ciki har dana Kiri wato Kiri dam,da sau tari sukan tunbutso,wanda kawo yanzu ma ba’a samu gargadi ba tukunna daga hukumomin kasar Kamaru,na ko shin za’a sako ruwa daga madatsar Lagdo,ko kuma a’a,wanda kuma lokaci ne kawai ke iya tabbatarwa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ambaliyan Ruwa Ya Yi Barna a Jihar Adamawa - 3' 03"