Ambaliyan Ruwa Ya Kashe Mutane Fiye Da Dari 350 A India

Yadda ake ceto mutane daga ambaliyan ruwa a india

Yawan mutanen da suka mutu a yankin Kerala a kudancin India da ambaliyan ruwa ya addaba sun dara 350 yayinda wasu daruruwa suka rasa muhallansu

Yawan mutane da suka mutu a jihar Kerala a kudancin kasar Indiya ya zarce dari uku da hamsin a yayinda dubban masu aikin ceto ke ci gaba da neman mutane a yankunan da ambaliyar ruwa ta yiwa barna jiya Lahadi.

Al’amarin dai ba kyau a jihar dake gabatar teku, sananiyar wajen yawon bude ido, inda kuma koguna, da madatsun ruwa suka batse a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, yayi awon gaba da hanyoyi da kuma gidaje.

Fiye da mutane dubu dari takwas sunyi hasarar matsuguninsu, yanzu suna zaune a sansanonin da aka kakkafa a jihar, al’amari kuma take tada tsoron bular anobar cututtukan da ake dauka ta ruwa mara kyau kamar kwalera da gudawa.

An kara kaimin aikin ceto da taimakawa, a yayinda bala’in ya bazu, kuma ana ci gaba da samun kiraye kirayen neman taimako daga mutane da suka makale akan rufin gidajensu a kauyukan da suke cikin lungu.

A wasu kauyukan ma, ambaliyar ruwan ta kai tsawon mita uku harma ta shiga cikin wasu gidaje.