Dimbin jama'a sun tsere daga gidajensu daga unguwar Natako cikin birnin Lokoja fadar gwamnatin jihar Kogi sanadiyar ambaliyan ruwa da ya soma mamaye unguwar tun daren jiya.
Unguwar na kan hanyar da ta ratsa jihar Kogin zuwa kudu maso kudancin Najeriya.
Wasu mazauna unguwar irin su Dr. Umar sun ce ruwan na gudu da karfi kuma duk abun da ya tarar kan hanyarsa yana tafiya dashi. Wani yace ruwan ya tsayar da motoci fiye da awa uku basu iya wucewa su nufi kudanci ko arewacin kasar ba. Suna mai cewa abun da ya faru bai taba aukuwa haka ba.
Gidaje da yawa ne lamarin ya shafa amma har yanzu babu alkalumma sai hukumar dake da alhakin yin kidigdiga ta fitar da bayani. To sai dai babu hasar rayuka.
Jami'an bada agajin gaggawa na cigaba da bada agaji, musamman mafaka ma wadanda lamarin ya rutsa da gidajensu. A wani bangaren kuma gwamnatin jihar ta dukufa wajen wayar da kawunan jama'a akan hadarin dake tattare da zama a wannan unguwar a daidai wannan lokacin.
Onarebul Ohinoyi Sha'aibu mataimakin gwamnan jihar na musamman akan harkokin kiwon lafiya yace sun sha ba mutane shawara akan unguwar tare da yi masu gargadi kada su yi gini kan hanyar ruwa.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5