Al'ummomin Madagali Da Michika Sun Bukaci Shugaban Kasa Ya Ziyarcesu

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Ziyarar Shugaba Buhari zuwa Dapchi domin jajantawa iyayen da 'yan Boko Haram suka sace 'ya'yansu ya sa al'ummomin Madagali da Michika kiran shugaban ya ziyarci yankunansu inda suka ce kungiyar Boko Haram ta sace matansu da yawa tare da daruruwan 'ya'yansu

Yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar gani da ido jihar Yobe game da batun yan matan makarantar Dapchi da yan bindiga masu tada kayar baya na Boko Haram suka yi awon gaba da su,wanda kawo yanzu ba’a san inda suke ba,suma al’ummomin yankunan Madagali da Michika da kuma Gwoza sun bukaci shugaban na Najeriya da ya kai irin wannan ziyarar yankunan.

Su na ganin ziyarar zata bashi damar sanin halin da iyayen yankuna ke ciki sakamakon yawan kwashe masu matansu da 'ya'yansu da Boko Haram suke yi. Sau tari mahukumtan jiharsu basa bayyana irin matsalolin da suke ciki. Kodayaushe 'yan Boko Haram suka ga dama suke shiga kauyukansu su kwashe mutane.

Mr Adamu Kamale dan majalisar wakilan Najeriya ne yace kawo yanzu akwai matansu da kuma daruruwan yara da yan Boko Haram suka sace,to amma har yanzu hukumomi a Najeriya basa maganarsu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Al'ummomin Madagali Da Michika Sun Bukaci Shugaban Kasa Ya Ziyarcesu - 1' 44"