Gwamnan yace akwai maganar inganta ainihin noma a Auyo inda aka ce za'a fadada aikin kuma an soma amma ba'a cigaba ba. An yi alkawarin za'a sa kudi kamar nera miliyan dubu goma zuwa ashirin wanda har yanzu ba'a cika ba.
Abu na biyu an ce za'a yi filin jirgin sama na dauka da saukar da kaya wato "Cargo Airport" a turance. Guda shida aka ce za'a yi a Najeriya cikinsu aka ce za'a yi daya a Dutse. Dalili ke nan yace sh zai fara nasa daga baya a biyashi.
Na uku hanya da ta taso daga Gaya zuwa Jahun zuwa Kafin Hausa hanyar tafi shekara ashirin bata da kayau. Gwamnan yace ya gayawa shugaban kasa da mataimakinsa. Akwai maganar fadada ruwan Dutse domin nan da shekara hamsin Dutse zai kasance cikin manya manyan biranen Afirka. Yace an yi masa alkawarin basa gudummawa.
Akwai kuma matsalar kwararowar hamada. Yace duk wadannan abubuwa aka yi ma su mutanen Jigawa alkawari. Yakamata a gane babu wani da suka hana takara. Duk Najeriya kowa nada 'yanci yayi takara. Amma maganar ita ce sun sa adashi a a dubu biyu da sha daya. Adashin suke so a biyasu. Idan aka biyasu adashin to 2015 kafin su sake zubawa zasu so su sani menene za'a yi masu.
Idan an bayyana masu idan kuma sun gane zasu yi, idan kuma basu gane ba ba zasu yi ba.
Amma mutane na cewa Jigawa ta ki bada hadin kai ne akan tsayawar takarar shugaba Jonathan saboda shi gwamna Sule Lamido na muradun zama shugaban Najeriya a zabe mai zuwa.
Gwamnan yace a fada domin akwai siyasa ta shegantaka. Yace an sha zaginsa. An kirashi kirista, fasto, arne. Yace ya sha zagi domin jam'iyyar.
To shin ko da gaske ne gwamna Sule Lamido zai shiga takarar neman zama shugaban kasa a zabe mai zuwa a karkashin inuwar PDP, yace kawo yanzu shi bai ce zai shiga takara ba. Idan yace zai shiga takara yana iya yi domin Najeriya kasa ce ta kowa da kowa kuma duk wanda ya ga dama na iya shiga takara. Amma ya godewa masu son ya fito ya shiga takara. Suna sonsa kuma ya godewa Allah har ma ana ganin ya dace ya tsaya zabe. Yace amma su a siyasa akwai yadda suke bin al'adunta wadda kuma sai sun gama da kansu su na gida a siyasance. Akwai matakai na jam'iyya tun daga kananan hukumomi zuwa jiha da kasa gaba daya. Saboda haka a cigaba da yin addu'a Ubangiji ya tabbatar da abun da ya fi alheri ga kasar.
Akan wanda zai gajeshi gwamnan yace Allah da yayishi shi zai yi wani, shi ne kuma ya san wanda zai kawo ya maye gurbinsa amma bashi gwamna ba.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5