Al'ummar Igbo din dake jihar Neja sun kira taron manema labarai inda shugabansu a jihar Chief Ezegbu Emmanuel ya bayyana cewa matsayinsa akan lamarin shi ne kira ga gwamnatin Najeriya da ta hau teburin tattaunawa maimakon yin anfani da karfi.
Akan fafutikar da wasunsu keyi na ganin an kirkiro Biafra daga tarayyar Najeriya Chief Emmanuel yace babu mutumin Igbo da ya san abun da ya faru lokacin yakin basasa da zai yi mafarkin sake shiga irin wannan yakin ba.
Ita gwamnatin jihar Nejan ta yi maraba da matakin da al'ummar Igbon suka dauka. Jibril Baba Ndace kakakin gwamnan jihar Neja yace gwamnan yana goyon bayan mutanen Igbo dake zaune a jihar.
Ranar 12 ga wannan watan 'yan kabilar Igbo din dake Neja zasu gudanar da wani gangami da suka sanya ma suna "macin zaman lafiya" a garin Suleja.
A nasu bangaren majalisar limaman jihar Neja sun ce sun dukufa wajen bayyanawa al'umma mahimmancin furta kalamun hada kan jama'a a daidai wannan lokacin.
Sakataren majalisar limaman Imam Faruk Abdullahi yace basu ji dadin kalamun shugaban kungiyar Kiristocin Arewa ba Bishop Matthew Hassan Kukah.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5