Garuruwan da aka fi zubar da jini sun hada da Lafiya, Obi, Keana, Awe, Nasarawa Eggon da wasu sassan Wamba.
Shugaban matasan kungiyar al'adun gargajiyan Eggon reshen Abuja Yahaya Suleiman Oshanduka shi ya karanta jawabin matsayin kungiyar akan rikicin jihar.
Rikicin wanda ya dauki hankalin duniya watan Mayun bara inda ma 'yansanda da dama suka rasa rayukansu a wani kwantan bauna da al'ummar Eggon tayi masu yayin da suke kai samame akan tungar shugaban matsafan Mbatse na kabilar wato Baba Alakio.
Yanzu dai Baba Alakio ya juye siyasa ko yin kokarin karbar madafin iko daga hannun Gwamna Umar Tanko Al-Makura.
Oshanduka ya cigaba da cewa mutanen Eggon su ne suka ba gwamna mai ci yanzu kuri'arsu har ya samu ya hau kan karagar mulki. Kodayake ba lallai ba ne mutumin Eggon ya zama gwamna amma rikicin nada nasaba da siyasa. Yace maganar addini ma bata taso ba. Yace su suna son su zauna lafiya da kowa domin basu saba da yin rikici ba
Mr Sule dattijon kabilar Eggon yace su ne suka fi jin jiki. Duk rikicin akan yare daya ake yi wato Eggon ne. Wai har an kama wani Abdullahi Bundi a gidan Gambo. Yace wasu yare suka kawosu domin su kone gidajen Eggon.
Tsohon gwamnan jihar Abdullahi Adamu na fatan kura zata lafa. Yace akwai wadanda suka lashi takobi basa son zaman lafiya da kowa sai nasu jinsin. Idan mutane suka goyi bayan abun da gwamnati keyi nan da dan lokaci za'a samu zaman lafiya.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5