Al'ummar Bama Sun Roki Gwamnatin Tarayya ta Kwato Garinsu daga Hannun 'Yan Ta'ada

Wasu 'yan gudun hijira daga Bama

Ganin yadda aka kwato kananan hukumomin Maiha da Mubi daga hannun 'yan ta'ada al'ummar Bama sun koka su ma a kwato masu yankinsu.

Shugaban riko na karamar hukumar Bama dake jihar Borno Alhaji Modu Alhaji Ari Gujja ya kira gwamnatin tarayya ta yiwa Allah ta kwato garin Bama daga hanun 'yan Boko Haram.

Garin Bama na cikin garuruwan da 'yan Boko Haram suka yi kaka-gida yau fiye da watanni biyu. Aika-aikar 'yan Boko Haram ya tilastawa mutane da dama barin garin. Wasu ma sun tsallaka zuwa kasashen ketare kamar su Kamaru, Chadi da Nijer.

Mafi yawan al'umman Baman suna kokawa ne akan rashin jin duriyar 'yanuwansu bayan da kungiyar Boko Haram ta tarwatsasu. Wadanda suka makale a garin Baman babu yadda za'a iya magana dasu domin babu wayar sadarwa kuma zuwa garin tamkar kama hanyar zuwa gidan mutuwa ne.

Shugaban karamar hukumar Baman yace tunda gwamnatin tarayya tayi ikirarin sake kwato garin Mubi su ma yakamata a ce an kwato nasu garin wanda aka kama tunda dadewa kafin Mubi ko Maiha.

Yawancin jama'ar Bama din dake Maiduguri suna cikin sansanoni guda hudu ne. Shugaban karamar hukumarsu yace gwamnatin Borno da wasu sun taimaka masu to amma zama a sansanin 'yan gudun hijira bashi da dadi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Al'ummar Bama Sun Roki Gwamnatin Tarayya ta Kwato Garinsu daga 'Yan Ta'ada 3' 29"