Wasu kungiyoyin dake fafutika da cin hanci da rashawa a Najeriya na bukatar shugaba Buhari da ya kula da wasu kusa dashi da ake ganin suna da bunu a tsuliyarsu.
Alhaji Abdulkarim Dayabu shugaban rundunar adalci a Najeriya ya bukaci a yi takatsantsan wurin zakulo wadanda zasu yi aiki da shugaban Najeriya domin a gujewa irin kurakuran baya.
Ya kira shugaba Buhari ya dubi irin mutanen da zai yi tafiya dasu domin wadanda ya yi tafiya dasu da sun yaudareshi. Misali wadanda suka goyi bayansa lokacin da ya zama shugaban mulkin soja su ne suka juya suka yi mashi juyin mulki suka ajiyeshi a kurkuku wata da watanni kana suka lalata komi.
Shugaba Buhari wanda ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa musamman a ma'akatar man fetue yace a kowace rana ana sace gangan mai fiye da dubu dari biyu da hamsin.
Alhaji Muhammad Samaila Gobir mai sharhi kan harkokin yau da kullum na ganin yunkurin yaki da cin hanci da rashawa zai taimaka ainun. Idan an kwato kudaden zasu taimakawa shugaban kasa ya fara aiki na gaggawa da mutrane ke bukata. Zai kuma taimakawa tattalin arzikin Najeriya. Yin hakan zai tsorata mutane su gujewa yin sata nan gaba.
Wani Abba Yahaya yace wasu sun canza duk da cewa ba canzasu aka yi ba saboda sun ga shugabancin kasar ya canza. Tunda an samu shugaba mai adalci mutane sun soma kimtsa halayensu saboda abun da ka iya biyo baya.
Daga bisani wasu na ganin yaki da cin hanci da rashawa ya hada da jami'an tsao masu karban akan hanya wadanda suka tatse mutane.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5