Alkali Ya Sake Dakatar Da Dokar Trump Ta Hana Baki Shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump, cikin fushi ya yi alkawarin zai je har gabar kotun kolin Amurka idan hakan ya zama wajibi, bayan wani alkalin wata babbar kotun Amurka a Hawaii ya jinkirta fara aiki da dokar wani rukunin mutane zuwa Amurka a umarnin da alkalin ya bayar jiya Laraba, sa'o'i kafin dokar ta fara aiki.

Alkali Derrick Watson, a hukuncin da ya bayar yace, lauyoyin gwamnatin jihar Hawaii sun gabatar da "hujjoji d a suka nuna cewa idan kotu bata han aiki da dokar ba, hakan zai iya jahar illa mai tsanani."

Shugaba Trump ya gayawa magoya bayansa a birnin Nashville na jahar Tennessee sa'o'i bayan hukuncin d a alkalin ya bayar cewa, "hadarin yana nan bayyane, ga dokar ita ma a bayyane, bukatar dokar shugaban kasan da na bayar ita ma gata bayyane," ya kara da cewa yana da ikon bari ko hana wand a zai shigo kasannan , domin kare Amurkawa.

Shugaba Trump ya zargi kotun gunduma dake Hawa'ii ya wuce makadi da rawa, yace "zamu ci gaba da wannan share har inda ya tsaya."

A halin da ake ciki kuma, shugabannin kwamitin kula da harkokin leken asiri a majalisar wakilai ta Amurka, sun fada jiya Laraba cewa zuwa yanzu ba su ga wata shaida da zata gaskanta ikirarin shugaban na Amurka Donald Trump yayi cewa, tsohon shugaban Amurka Barack Obama, yasa a yi masa kutse, gabannin a zaben Amurka da aka yi cikin watan Nuwambar bara.