A taron bitar aikin alhazan Najeriya dubu 76 da aka saba yi bayan an kammala aikin hajjin gabanin mika rahoton hukumar alhazan ga gwamnatin Najeriya, shugaban hukumar ya amsa tambayoyi tare da rufewa da addu'a.
A taron an yiwa alhazai 33 da suka rasu yayin da suke yin aikin ibada a kasa mai tsarki. Dr Ibrahim Kana daga ma'aikatar kiwon lafiya kuma jagoran likitocin alhazan ya tabbatar da rasuwar alhazai 33. Yace sun zauna sun duba menene sanadiyar rasuwar tasu. Kashi hamsin zuwa sittin na alhazan da suka rasu ciwon zuciya da makamantansu suka jawo rasuwarsu.
Duk alhazan da suka dawo sun dawo cikin koshin lafiya. Babu ebola a can kuma su ma basu taho da ebola ba.
Shaikh Saidu Hassan Jingir yana ganin alhazan Najeriya suna bin ka'ida. Yace idan alhazan Najeriya na wa'azi akwai ilimi ciki. Yace da, da zara rana ta kama sai mutane su dinga barin hawan arfa to amma yanzu lamarin ya canza domin ilimi ya ishesu sun gane cewa ba'a barin arfa sai bayan rana ta fadi. Wasu idan sun tsinci kudi masu yawan gaske sai sa kai inda za'a sanar domin maishi ya amshi abunsa.
Akwai wasu korafe korafe musamman na rashin samun zuwa Madina akan lokaci ga alhazan Gombe da rashin isowar kayan wasu alhazan daga kamfanin Kabo da kuma jibgin wasu kayan da suka wuce ka'ida da wasu alhazan jihar Nasarawa su 500 suka yi da ake sa ran isowarsu daga Sadiya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5