Algeria Ta Tasa Keyar Wasu ‘Yan Nijar Komawa Kasarsu

Wasu 'yan Nijar da suka dawo gida

Duk da kiraye kirayen da gwamnatin Jamhuriyar Nijar keyi na cewa ‘yan kasar su zauna kasarsu su daina balaguro zuwa wasu kasashen, musamman kasashen dake makwaftaka da ita, har yanzu ‘yan kasar basu daina ba lamarin da ya kai ga kasar Algeria ta koro wasunsu daga kasarta

Duk da kiraye kirayen da gwamnatin Nijar da kungiyoyin duniya keyi kan daina tafiyar ci-rani, lamarin bai sauya ba.

Yanzu haka, kasar Algeria ta maida daruruwan wasu ‘yan Jamhuriyar Nijar zuwa kasarsu, kuma yanzu hakan sun fara isa a garin Agadez.

A cewar wasu daga cikin wadanda aka maido gidan, an kwashesu ne da motoci alatilas su koma kasarsu. Mutanen Nijar din sun fito ne daga jihohi daban daban.

Jami’in dake kula da wadanda aka dawo dasu Nijar dake aiki a Agadez yace damuwarsu yanzu ita ce inda zasu ajiye mutanen da suka dawo din, wadanda yawansu ya kai 246, saboda ba’a kammala gina tantunan da ake gina musu ba, sannan kuma ga matsalar rashin abinci da ruwan sha.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Algeria Ta Tasa Keyar Wasu 'Yan Nijar Komawa Kasarsu - 3' 12"