Rashida Ismail malamar asibiti a Kanon Nijeriya ta ce da farko ta so ta karanci community health, wato malaman jinya da suke shiga karkara sakamakon cin jarabawar da tayi sosai sai aka kaita fannin pharmacy wato magunguna.
Malama Rashida ta ce da farko da ta fara karatun harkar magunguna ta tsorata sakamakon yadda ‘yan uwanta suke kururuwar cewar karatun na da wuya, ta ce da jajircewa ta kammala ba tare da ta fuskanci wasu matsaloli ba.
Ta kara da cewa tun lokacin da ta fara aiki ta fuskanci wasu kalubale da dama kasancewarta mace mai aure ga matsala ta gida da iyali ga kuma harkar aiki na sibiti du kuwa da cewar mai gidanta ya bata damar yin aiki cikin sauki.
Ta ce babban abin sha’awa a wannan aiki nata dai shine tana taimakawa ‘yan uwanta mata mussamam ma afanni lafiyarsu.
Daga karshe ta ce ilimin diya mace na da matukar alfanu, tare da jan hankalin iyaye da su baiwa ‘ya’ya mata dama samun karatun boko domin taimakawa a wasu sassa na rayuwa.
Your browser doesn’t support HTML5