Alexis Sanchez Zai Koma Manchester United - Solskjaer

Kocin kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, ya goyi bayan dan wasan kasar Chile da cewar zai sake dawo wa da karfinsa, idan ya koma taka leda a Old Trafford a kakar wasa mai zuwa.

Solskjaer ya tabbatar da cewa Alexis Sanchez zai dawo kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, bayan kammala wa’adin zaman shi a kungiyar Inter Milan a matsayin aro.

Dan kasar Chile din ya koma kungiyar ta Italiya ne a yarjejeniyar aro a watan Agustan bara, amma har yanzu yana da sauran shekaru biyu na kwantirakinsa don ci gaba da taka leda a kulob din sa na Old Trafford.

Sau daya kawai dan wasan ya zura kwallo a raga, a cikin wasanni bakwai da ya bugawa Inter Millan, saboda raunin da ya samu wanda ya hana shi ba da wata gudummawa sosai.

Dan wasan mai shekaru 31 da haihuwa, tun a shekarar shi ta farko a kungiyar Man. United, ya fuskanci matsaloli saboda ya kasa nuna wata bajinta, irin wadda ya nuna akai-akai yayin da ya ke kungiyar Arsenal.

Amma Solskjaer ya tabbatar da cewa har yanzu yana da makoma a kulab din.

Kocin na Man. United ya fada a taron manema labarai ranar Talata cewa: "Alexis zai dawo kungiyar a lokacin bazara, kuma zai tabbatar wa duniya cewar yana tare da kungiyar dari-bisa-dari."