Alee-gee; Yawancin Mawakan Hausa Na Zamani Sun Fi Raja’a Da Wakokin Soyayya

Aliyu Inuwa wanda aka fi sani da Alee Gee, mawakin gambara wato hip-hop ya ce ya zabi fagenne domin sauya salon waka da matasa ke yi domin yawancinsu sun fi raja’a da wakokin soyayya ko nanaye a ta bakinsa.

Matashin ya kara da cewa yana isar da sakoninsa ta waka ne da kuma salon gambara wato hip-hop, ta hanyar daukar dabi’un al'umma domin nusar da su, alal misali Alee-gee ya ce yakan dauki matsaloli kamar na ‘Zato, inda ya ce akwai dabi’ar nan ta mutane ta yawan zaton dabi’un wasu ba tare da sun san ainihin abinda ya faru ba kuma ba tare da sun bincika ba.

Ya ce ban da wannan akwai matsalolin da matasa ke fama da su kamar karbar bashi ko na yawan kashe kudi da matasa ke yi ba tare da sun la’akari da manyan bukatunsu yadda ya kamata ba, haka kuma suna kashewa batare da sun kassafta bukatu bi da bi ba.

Alee-gee, ya ce babban kalubaen da suke fuskanta a yanzu shi ne, mawaki shi ke da alhakkin rubuta wakokinsa, ya nada a faifai ya kuma tallata kansa wanda a zahirance ba hakan yakamata ya kasance ba.

Daga karshe Aliyu Inuwa, ya ce ya gamsu da sana’arsa domin yana samun bayanai abinda yake yi ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani domin gyara wasu kurakuran da masoyyansa suka aiko masa.

Your browser doesn’t support HTML5

Alee-gee; Yawancin Mawakan Hausa Na Zamani Sun Fi Raja’a Da Wakokin Soyayya