Wani rubutaccen bayanin da ya shigo hannun gidan rediyon nan na Muryar Amurka, VOA, ya nuna cewar shugaban Koria ta Arewa Kim Johg Un, bai da niyyar wargaza shirin shi na kera makamai masu linzami.
Wanda wannan matsayin ya sabawa tunain da gwamnatin Amurka ta shugaba Donald Trump ke yi na cewar Koria din zata wargaza shirin ta na kera makaman.
Takardun sun kunshi darussan da aka shirya na koyar da manyan sojojin Koriyar ne, wadanda aka fitar dasu gabanin taron da aka yi tsakanin shugaban Koriya din da Trump.
Takardun sun bayyana karara cewa, Kim ya kalli wannan taro na Hanoi a matsayin wata dama ta samar da yarjejeniyar karshe, wacce zata nunawa duniya, kasarsa yanzu ta shiga jerin gwanon “kasashen duniya da suka mallaki makaman kare dangi na nukiliya.”