Al'ummar Kirista A Duniya Baki Daya Sun Fara Bukukuwan Ista

Kowane shekara mabiya addinin Kirista na kwoikwoyon yadda Bishara ta bayyana Yahudawa suka giciye Yesu Almasihu.

A yau, ranar da ake kira 'Good Friday', wato Jumma'a mai kyau, rana ce da mabiya addinin Kirista ke imanin an giciye Yesu Kristi, kamar yadda Allah ya tsara, domin ya kasance mai ceton dukkan bil'adam, daga shiga jahannama.

JOS, NIGERIA - Rabaran Yusufu Turaki, Farfesa ne a ilimin tauhidi, yace lokaci ne da mabiya Yesu Almasihu zasu yi bishara zuwa ga tuba.

Bikin Istan na bana ya zo ne a lokacin da ake samun tashe-tashen hankula da kashe-kashe.

Farfesa Yusufu Turaki ya bukaci shugabanne da daukacin al'umma, musamman a Arewacin Najeriya, su sanya matakan samadda zaman lafiya.

Duk da matsin rayuwa da al’ummar Najeriya ke fama da shi, wassu mabiyan na Yesu Almasihu sun bayyana fata nagari.

A cewar Malama Jummmai Tambaya duk da tsadar kayayyaki, Krista su tuna da ceto da suka samu.

Hakazalika, Malam Danjuma Dickson Auta yace sun yi addu'oin godiya ga Allah da ya nuna musu wannan rana mai muhimmanci a addinin Kirista.

Madam Miriam David Philip tayi fatar Allah ya kawo saukin rayuwa.

A sakonsa na Ista, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya jinjina wa 'yan Najeriya bisa hakurinsu a cikin watannin mulkinsa, wanda yace gwamnatinsa na aiki tukuru don daidaita lamura da samun ci gaba.

A saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Al'ummar Kirista Sun Fara Bukukkuwar Ista