Kawo yanzu dai hukuma ko Masarautar Sarkin Musulmi ba su ce uffan ba, duk da faifan bidiyon da ke nuna basaraken yana dab da rasa ransa.
An dai sace basaraken ranar 27 ga Yuli 2024, yau mako uku da kwana biyu.
A faifan bidiyon, ana ganin basaraken daure da sarka jini ya zuba a gaban tufan da yake saye da ita, basaraken ya yi bayani a kan ukubar da yake sha hannu wadanda suka yi garkuwa da shi, tare da dansa, har ta kai ga an yi musu alkawalin kisa in ba a biya kudin fansarsu ba.
Wannan bidiyon dai a cewar iyalansa ya tayar musu da hankali ganin har yanzu mahukunta ba su dau wani mataki ba wajen fitowarsa har yana dab da barin duniya.
Har iyau iyalan na sa sun nemi agaji daga jama'a don samun kubutar da mahaifin su.
A halin da ake ciki a garin Sabon Birni wannan faifan bidiyon ya tayar da hankulan talakawa a cewar wani mutumin garin Muhammad Abdullahi Gobir.
Kawo yanzu dai ba hukumar da ta fito a bayyane ta yi magana a kan basaraken duk da fitowar wannan faifan bidiyon, duk da yake Mataimakin Gwamanan jihar, Idris Muhammad Gobir, dan asalin Sabon Birni, basarakensu ne ke fuskantar barazanar mutuwa hannu 'yan bindiga din.
Duk da yake gwamnan Sakkwato yana cewa gwamnatinsa na kokari wajen samar da tsaro, amma dai har yanzu mutanen Sabon Birni da wasu sassan gabashin Sakkwato suna cikin mummunan yanayi.
Ga rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5