Al'amura Sun Fara Daidaita A Jihar Filato

Jos, Nigeria

Jama'a sun bude wuraren kasuwancinsu gami da cigaba da harkokinsu kamar kullum.

Al’amura sun fara daidaituwa bayan rikicin da ya nemi kunno kai a Jihar Filato, bayan kashe wasu mutane 15 yan bindiga sukayi a Rukuba Road dake cikin garin Jos.

Duk da kone konen ababen hawa da ofishin Yan sanda da wasu matasa sukayi a jiya, a yau Jama’a sun bude wuraren kasuwancinsu gami da gudanar da harkokin su kamar kullum.

Jami’an tsaro a Jihar sun ce sun shawo kan lamarin. Ga Zainab Babaji dauke da cikakken rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Cigaban Zaman Lafiya A Jihar Filato