Wani rukunin mutane da wani kusa a jam’iyyar GERB, kuma dan takarar jam’iyyar, tsohon Minister Boyko Borisso yayi nasar samun kaso 16.5% na kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a ranar Lahadi, yayin da jam’iyyar dake ra’ayin tsarin kasashen yamma karkashin jagorancin jam'iyar PP, ya samu kaso 24.9% na kuri’un da aka kada a bisa alkaluman sakamakon kaso 96% na zaben da aka tattara.
Jami’iyyar Nationalist Rival, da ke goyon bayan Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a yakin da ake yi da Ukraine ne ta zo ta uku da kaso 14.4% cikin dari, kason kuri’un da jam'iyar ta samu ya karu da kadan daga sakamakon zaben da aka gudanar na baya a watan Oktoba.
Jam’iyyar ‘yar Rurkiyya MFR ne ya kasance na 4 da kasop 13% cikin dari, sannan jam’iyyar Bulgarian Socialist Party wanda ya samo asali daga jam’iyyar ‘yan gurguzu ya samu kaso 9% cikin dari.
Dadaden tarihin rikicin siyasar Bulgaria wanda rashin jituwa tsakanin shugabannin manyan jam’iyyun siyasar kasar tuni ya tursasawa kasar jikirta anniyar kasar ta rungumar amfani da euro kana, har ya zuwa yanzu, kasar bata amince da kasafin kudin bana ba.
Rashin tabbacin ya kuma hana Bulgaria cin moriyar kudaden tada komadar tattalin arzikin da EU ta tanadar bayan kullen korona, sannan, masu sharhi da masu kada kuri’a suna tsoro kada rashin mai nasara a zaben ranar lahadi ya kai ga gudanar da wani zabe nan gaba cikin wannan shekarar.