Akwai Wadanda Aure Ya Haramta Garesu: Daurawa

A bisa mahauwarar da ake yi akan batun aure a jihar Kano, na neman hana mazajen da basu da kafin rike mata biyu kara mata wata matashiya mai suna Shamsiyya Bello, ta jinjinawa mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, a bisa kudurin da ya mika ake mahauwara akai na batun aure.

Tace mazajen da dama su kan auri mata biyu, uku ko kuma hudu amma daga bisani dawainiyar gidan wanda suka hada da abinci situra da makarantar yara duk kan iyaye mata yake komawa.

Ita ma Zahrau Muhammad, cewa tayi idan hakar ta cimma ruwazai taimaka wajan samun yara masu tarbiya da kuma rage yara marasa ji masu yawo loko loko

Ita kuwa Firdausi Lawal, cewa tayi wannan kudiri yayi daidai domin kuwa duk namijin da bashi da karfin tattalin arzikin da zai rike mata biyu ba, ba zasu rika Karin aure ba da kuma haifar da mutuwarsa akai- akai.

Shugaban hukumar Hisbah, Mal Aminu Ibrahim yace akwai wadanda musulunci ya haramta masu yi aure domin wasu dalilai domin jin wadannan dalilai sai a saurari sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Wadanda Aure Ya Haramta Garesu: Daurawa - 2'47"