Akwai Tukwuici Ga Wanda Ya Gano Mutumin da Ya Kashe Limamin Wani Masallacin New York

Wani ke dauke da kwatankwacin hoton wanda ya kashe limamin masallacin Ozone Park dake New York

Wata kungiya mai fafutukar kare adddinin Islama, ta yi tayin bayar da tukwicin dala dubu goma, ga duk wanda ya taimaka wajen gano wanda ya kashe limamin wani masallacin birnin New York da wani na hanun damansa.

An harbe Imam Maulana Akonjee mai shekaru 55 da abokinsa Thara Uddin mai shekaru 64, bayan da suka fito daga masallaci akan wani titin birnin na New York a ranar Asabar.

Majalisar Malamai ta Amurka, ta ce za ta bayyana wannan sanarwa a hukumnce a yau Litinin.

“Muna fatan wannan tikwici zai kai ga gani cafke da kuma hukunta wanda ya aikata wannan danyan aiki. Muna kuma fatan za a fadi dalilinsa na aikata kisan.” In ji babban darektan Majalisar Malaman, Nihad Awad.

‘Yan sanda dai sun saki zanen mutumin, mai bakin gashi, sanye da tabarau ko kuma gilashi, kuma ya zuwa yanzu ba su ambaci dalilin da ya sa aka harbe Malaman ba.

Mahalarta masallacin da suka taru bayan an kashe limaminsu

Sai dai masu fafutuka a kusa da masallacin na Al Furqan da ke kusa da wajen wani shakatawa a yankin Queens, sun ce harin alama ce ta nuna kiyayya da kyama.