Akwai Sauran Rina A Kaba, Wane Klob Zai Lashe Gasar UEFA Na Bana?

Duk da gagarumar nasara da Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta samu a wasan cin kofin zakarun Turai Uefa zagaye na biyu, bayan da ta lallasa Schalke O4 kwallaye 7-0 jimilan kwallaye 10 da 2 a wasanni biyu.

Mai horar da kungiyar ta Manchester City Pep Guardiola, ya bayyana shakku kan cewa kungiyar tasa za ta iya lashe kofin gasar Zakarun Turai na bana a
karon farko.

Kocin ya fadi hakanne kasan cewar wasu daga cikin masu sharhi kan kwallon kafa suna hasashen cewa City na daga cikin kungiyoyin da ake ganin za su iya lashe gasar ta bana.

Guardiola ya bayyana mamakinsa kan yadda Manchester United ta fitar da Paris-saint German daga gasar, da kuma yadda Ajax ta fidda Real Madrid, inda ya ce fitar da manyan kungiyoyin, ba shine sharar fage ga Manchester City na kawo mata saukin damar lashe zakarar nahiyar Turai a bana ba.

Manchester City a yanzu haka ta kai ga wasan zagaye na gaba wanda kungiyoyi takwas zasu fafata a matakin wasan daf da na kusa da na karshe (Quarter Final).