Akwai Rashin Gaskiya Wajen Biyan su Albashi.

Fiye da ma’aikatan wucin gadi 2600, ne Gwamnatin jihar Kano ta sallami bayan sun kwashe shekaru da dama suna aiki a hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar, sai dai kungiyar kwadogo ta najeriya reshen jihar Kano ta kalubalanci matakin.

Kwamishinar yada labarai na jihar Muhammad Garba, ne ya bayyana haka a wata hira da wakilin muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari a birnin Kano.

Yan mai cewa wandannan ma’aikata an lura an gani cewa basu gudanar da aikin su kuma an lura cewa akwai harkar rashin gaskiya wajen biyan su albashi.

Ma’aikatan da wani lamari ya shafa sun ja hankalin Gwanatin ta Kano game da mahimmancin wanzar da adalci a gare su, yanzu masamman ta la’akari da cewa yanzu haka sun kwashe fiye da watani biyu kennan Gwamnati bata biyasu hakkokin su na kwadago ba.

Game da wannan batu shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, rashen jihar Kano Kabiru Ado Minjibir, yace kungiyar Kwadago ta dauki wannan abu da mahimmanci domin abun ne da ya shafi al’uma da dama.

Yace A mastayinsu na masu ruwa da tsaki tilas ne kungiyar ta jajirce a madadinsu domin ganin cewa wannan abu an yi shi cikin gaggawa da lumana.

Dangane da batun dauka ma’aikata, a matsayin wucin gadi kuwa shugaban yace kungiyar Kwadago ta Duniya ILO, wace Najeriya,na cikin ta haramta aiki na wucin gadi.