Akwai Kasashen Da Cutar COVID-19 Ba Ta Bulla Ba a Afirka - WHO

Yayin da dokokin hana zirga-zirga a Afirka ke nuna alamun sassautawa, masana kiwon lafiya sun bukaci a yi daidaito a manufofin kiwon lafiya don kiyaye tattalin arziki da rayuwar yau da kullun.

Rahotanni daga Afirka na nuni da cewa, jami’an lafiya a nahiyar sun yi nasarar shawo kan mahukunta wajen ganin sun dauki tsauraran matakan dakile yaduwar cutar coronavirus.

Kuma ana ganin hakan na da nasaba da yadda aka ga kasashen da ke kudu da Hamadar Sahara suke da mafi karancin adadin masu dauke da cutar a duk fadin duniya.
Sai dai duk da hakan, Daraktar Hukumar Lafiya ta WHO mai kula da yankin nahiyar Afirka, Dr. Mathshidiso Moeti ta ce har yanzu akwai sauran jan-aiki a gaba.

Moeti ta ce, “dangane da abin da ya shafi Afirka, muna ganin karin masu dauke da cutar, sannan mun fi damuwa da kasashen da ke yankin yammacin Afirka, inda ake ganin karin mutanen da ke harbuwa da cutar, idan aka kwatanta da sauran kasashen da ke nahiyar.”

Sai dai Daraktar ta ce, wani abin farin ciki shi ne, har yanzu akwai wasu kasashe da cutar ta COVID-19 ba ta bulla ba a nahiyar, ko da yake kasashe ne kanana kamar Namibia, Mauritania da kuma Seychelles, domin a cewarta, sun dauki matakan da suka dace tun lokacin da cutar ta fara bazuwa a duniya, matakin da ta ce, ya yi wa kasashen rana.