Mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Usman Mamman Durkwa wanda ya wakilci gwamna Kashim Shettima a bikin ranar ma'aikata da aka yi jiya , ya zanta da Muryar Amurka inda ya bayyana irin fahimtar juna dake tsakanin gwamnati da ma'aikatan jihar.
Yace jihar ta soma samun zaman lafiya kuma ya godewa jami'an tsaro da ma'aikata da suka ba gwamnati hadin kai. Ta dalilin ma'aikata jihar ta samu zaman lafiya saboda goyon bayan da suka ba gwamnati akan tantancesu da gwamnatin ta yi. Shugabannin ma'aikatan suna goyon bayan gwamnati dari bisa dari kan tantancewar.
Dangane da rashin biyan albashi mafi kankanci a wasu kananan hukumomin jihar mataimakin gwamnan yace ba laifin gwamnati ba ne kuma ba laifin ma'aikatan ba ne. Hallin da gwamnati ta shiga da yawan ma'aikatan suka haddasa hakan. Yace da zara gwamnati ta samu kudi zata biyasu. Ya kirasu su kara hakuri na dan wani lokaci.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5