Akwai Bukatar Wayar Da Kan Matasa Akan Siyasar Uban Gida - Yakubu Hashim

Yakubu Hashim

Yakubu Hashim, matashi mai gwagwarmayar kwato wa ‘yan uwansa matasa ‘yancin kai domin a dama da su a harka ta siyasar Nijeriya.

Ya ce suna bukatar wayar da kan matasa domin a daina siyasar uban gida ta hanyar cusa masu kishin kasa da daina kallon siyasa irinta sauran kasashe ba tare da anyi duba da tattalin arzikin kasa da dabi’unta kafin gudanar da siyasa yadda ya kamata ba.

Matashin ya ce hatta rikce-rikicen da ke wakana tsakanin kabilu a wasu sassan Nijeriya, za’a iya akanta su da yanayi na siyasa, inda yake cewa ya kamata a sauya yanayi na demokradiya a Nijerya.

Yakubu, ya ce kowacce jam’iyya na da tsarin tafiyar da jam’iyyar ta amma abin takaici shine yadda hukumar zabe ke sanya kudin sayen katin tsayawa dan takara wanda yake kudine masu tarin yawa da matasa basu da karfin mallaka dole ta sanya sai sunyi siyasar uban gida.

Dan haka ne ma suke yunkurin kaddamar da wata sabuwar jam’iyya mai suna SPN Socialist Party of Nigeria, wanda suke neman a amince masu amma har yanzu hakarsu bata cimma ruwa ba, domin hukumar zabe bata gama tantance su ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Wayar Da Kan Matasa Akan Siyasar Uban Gida - Yakubu Hashim