Akwai Bukatar Sauya Manufofin Tattalin Arzikin Najeriya

Koma bayan tattalin arzikin Najeriya na ‘kara lalacewa saboda wasu manufofi na gwamnatin Buhari da ribarsu zata bayyana ne a dogon zango.

Masanin tattalin arziki Usha’u Aliyu, yace rufe iyaka da hana shigo da abinci shine ya ‘kara ta’azzara lamura “ana noman an noma tumari sai kuma da kwandonsa ya koma Naira 300, saboda tsananin noman. Amma akwai wani yanayi ne da aka shigo wanda abu biyu ne suka haifar da hauhawar farashin.”

A cewar Usha’u abu na farko shine yanayin da gwamnati ta samu kanta na rashin kudin Dala, ta hana ‘yan canji kudaden da ake basu daga babban banki ‘kasa kuma ya shafi duk abubuwan da ake saya, domin kashi 70 na abin da ‘yan Najeriya suke amfani da shi wanda suka hada da riga rigar sawa da abinci da waya har magunguna daga kasashen waje ake fitowa da su. Abu na biyu shine rufe boda da akayi, kasancewar wasu ‘yan kasar sun dogara ne ga zuwa su sayo kayayyaki domin su samu riba.

Wani ‘dan siyasar APC Garba Tela, yace akwai bukatar sauya manufofin tattalin arzikin na gwamnatin ta Buhari.

Sai dai shahararren Malamin addinin Islama Sheik Yakubu Isa Katsina, yace gaggawa ba zata haifar da alkhairi ba, “ya zama wajibi ga duk ‘dan Najeriya mai hankali mai adalci yasan cewa wannan kunci da ake ciki sakamakone na mummunan jagoranci da shugabannin da suka gabata suka yiwa wannan ‘kasa.”

Rahotanni na nuna fitowar sabuwar shinkafa ya fara rage tsadar abinci da ake fuskanta musamman a yankunan karkara.

Saurari cikakken rahotan Saleh Shehu Ashaka daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Sauya Manufofin Tattalin Arzikin Najeriya