Shahararren dan wasan kasar Brazil Willian Borges da Silva ya bukaci a dauki kwararan matakai akan duk wani dan wasa da ya nuna halin wariyar launin fata, bayan wani lamari na nuna wariya da ya faru da dan wasa Taiso, a lokacin wasan da suka gwabza ranar Lahadin da ta gabata.
Duk da cewar sun yi nasara da ci 1-0, an ba dan wasan jan kati a lokacin da wasu 'yan kallo suka yi ta waken "wariyar launin fata" shima ya taya su yin wakar. Shakhtar da kocin kungiyar Luis Castro, sun fitar da wata sanarwa wadda suka bukaci hukumomi su dauki kwararan matakai akan duk wanda aka samu da nuna hali irin wannan.
Cikin jawabin sa gabanin wasan, Willian yace “wannan wani abun takaici ne” za kuma muyi duk abin da ya kamata don kawo karshen irin wannan halin, amma kungiyoyi da gwamnatoci na da muhimiyyar rawar da zasu taka don kauda irin wannan dabi’ar.
Dole a dinga daukar matakan kawo karshen hakan a dai-dai lokacin da lamarin ya faru, da kuma sanya matakai masu tsananai ga duk wanda aka samu da aikata irin wadannan halayen.