Akwai Bukatar Kawo Karshen Nau'ukkan Ayyukan Bauta A Afrika

A jamhuriyar Nijar kungiyoyin yaki da bauta sun gudanar da wani taron kwanaki 3, domin nazarin gudunmawar da zasu bayar wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel, sakamakon lura da cewar ana amfani da mutanen da ake bautarwa domin kai hare-hare.

Kwararru daga Jami’o'in kasashen Mali, Burkina Faso, Mauritania, Chad, Nijar da tsibirin Ile Maurice, da jami’ar Birminghham ta kasar Ingila, a daya gefen jami’an kare hakkin bil'adama ne ke halartar wannan taron, da kungiyar Timidria mai yaki da bauta ta shirya, da nufin zakulo sababbin hanyoyin tunkarar wannan matsalar, dake zama tamkar ana magani kai yana kaba, Malan Ali Bouzou shine magatakardan wannan kungiya.

A sakamakon lura da faruwar wasu abubuwan dake ta kara karfafawa ayyukan ta’addanci gwiwa a yankin Sahel, ya sa taron na birnin Yamai tunanin kafa wata kungiyar hadin gwiwa da ake kira G5 Excalvagisme, da nufin bada gudun mawa a wannan yakin, inji sakataren Timidria.

A karshen wannan taron dake kammala a yammacin yau Alhamis, wakilan kasashen dake halartar wannan taron, na yaki da bauta zasu fitar da wata sanarwa mai dauke da abinda ake yiwa lakabi da shawarwarin birnin yamai.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Kawo Karshen Nau'ukkan Ayyukan Bauta A Afrika 2'40"