Akwai Bukatar Hadin Kai A Zaben Gwamnoni Na Ranar Asabar

La’akari da matsaloli da tashe-tashen hankula da aka samu a zaben gwamna da ya gabata a jihar Sokoto, wanda yayi sandiyyar soke zaben runfuna 135, a cikin kananan hukumomi 22 na jihar, ya sa kwamitin wanzar da zama lafiya na kasa a karkashin shugabanci tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar, shirya wani taron yarjejeniyar tabbatar da gudanar da sake zaben cikin lumana a jihar.

Taron ya hada hancin dukkan masu ruwa da tsaki a sha’anin zabe, da shugabannin al’umma da na addinai, kazalika da kungiyoyi masu zaman kansu, da masu sanya ido akan zabe daga ciki da wajen Najeriya.

Da yake bita akan matsalolin da aka fuskanta a zaben na gwamna da ya gabata, kwamishinan hukumar zabe ta kasa a jihar Sokoto Sadiq Abubakar, ya zargi ‘yan siyasa a jihar, da hura wutar rikici, tare da neman mulki ido rufe, lamarin da yace ya kawo babban kalu-bale ga kokarin hukumar na shirya sahihi kuma ingantaccen zaben na gwamna cikin kwanciyar hankali a jihar.

A can baya dai kafin gudanar da zaben na gwamna, kwamitin na wanzar da zaman lafiya na kasa ya gudanar da irin wannan taron, inda ‘yan takarar gwamna suka rattaba hannu a yarjejeniyar bada hadin kai ga gudanar zaben cikin lumana.

Hukumar zabe ta ayyana zaben gwamna a jihar ta Sokoto da cewa bai kammala ba, sakamakon adadin Kuri’u fiye da dubu 70 da aka soke zabe a rumfuna 135, ya zarta adadin kuri’un da suka bambance tsakanin dan takarar PDP Aminu Waziri Tambuwal dake kan gaba, da na APC Ahmad Aliyu, wadanda kuma za’a sake zaben a jibi Asabar.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Hadin Kai A Zaben Gwamnoni Na Ranar Asabar 2'30"