Akwai Bukatar Garanbawul A Sha'anin Wasa A Najeriya

Sunday Akin Dare, Ministan Matasa da Wasanni

Ministan matasa da ci gaban wasanni na tarayyar Najeriya. Mista Sunday Dare, ranar Litinin da ta gabata, ya gana da mambobin Hukumar kula da wasan Kwallon kafa ta Najeriya (NFF).

Inda ya bukaci da a yi masa cikakken bayani game da ficewar kungiyoyin Najeriya daga gasar kwallon kafa.

Najeriya a bangarori daban-daban a wasan kwallon kafa bata samu tikitin halartar shiga ba da suka hada da gasar 'yan cikin gida (CHAN) da na Olympic da za a yi a Tokyo, haka kuma akwai gasar Wafu wadda ita ma Najeriya ba zata halarta ba.

A cikin ganawar da su ka yi wacce ta dauki tsawon mintuna 30, Ministan ya ba da umarnin cewa hukumar NFF, nada bukatar bai wa gwamnatin tarayya cikakken bayani game da abinda ya samu kungiyoyin kasar na rashin shiga gasar har sau hudu.

Dare ya ce yanzu lokaci ya yi da za a yi wa 'yan Najeriya bayani domin akwai bukatar daukar tsauraran matakai da bincike na gaskiya.

Ministan ya kara da cewar ba zai ce dole sai an samu nasara ba ko kadan, amman ana so gano batutuwa daban-daban na ko menene ya kamata ayi don magance wadannan batutuwan kwallon kafa a kasar.