Shugaba Akufo-Addo ya kiran ne ga shugabannin kasashen duniya, a taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya karo na 29 (COP29) da ke gudana a kasar Azerbaijan, inda ya kalubalance su da su motsa daga maganar fatar baki kawai zuwa daukar mataki na dakile matsalar sauyin yanayin duniya a aikace.
Shugaba Akufo-Addo ya jaddada cewa, karuwar sauyin yanayi, musamman kan al'ummomi masu rauni, na bukatar hadin gwiwa tare da aiki na hakika. Yace, akwai damuwa kwarai, idan aka yi la’akari da yawan tarukan sauyin yanayi, amma har yanzu babu wani kwakkwaran tsari na dakile matsalar. Yace: ‘A yau mun hadu ba kawai a matsayin shugabanni da masu tsara manufofi ba, amma a matsayin daidaikun mutane da muke son kasarmu da al'ummominmu na gaba. Mu bari taron COP 29 a nan Azerbaijan, ya nuna muhimmin canji daga tattaunawa zuwa tabbatarwa’.
Shugaba Akufo-Addo ya bayyana cewa, Ghana na samun ci gaba mai dorewa da burin rage hayakin da take fitarwa da tan miliyan 64 nan da shekarar 2030; Ghana ta dasa bishiyoyi miliyan 50 daga shekarar 2017 zuwa yau; Ghana tana tsarin ababan hawa masu amfani da wutar lantarki, don hanzarta canjin makamashi.
A hirar sa da Muryar Amurka, Mohammed Jafar Dankwabia, mataimakin daraktan bincike a Cibiyar Sauyin Yanayi da Samar da Abinci yace inda aka yi tattaunawar, nan ake bari sai sabuwar shekara a dora daga nan. Yace, kiran da shugaban kasar Ghana ya yi, shi ne suke kai cewa, ‘A tashi a yi aiki, a san yadda za a magance hauhawar zafi; rafi na bushewa, babu ruwan sama, kuma duka mun san cewa ayyukanmu ne suka kai mu ga haka’.
Sai dai masana kan yanayi da muhalli sun mayar da martani ga shugaban; suka ce wannan kira da ya yi, da kuma ababan ci gaban da ya ambata gwamnati ta yi kan kiyaye muhalli ba su bayyana yanayin da kasar ke ciki ba, idan aka yi la’akari da illar da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suka yi wa muhalli a kasar.
Ko-idinetar kungiyar tsaftace muhalli, Eco-Conscious Citizens, Awula Serwaa, da take mayar da martani kan jawabin shugaba akufo-addo, a kafar telebijin na TV3, tace:
Ina tunanin ko yana maganar wata kasa ne. Ana lalata dazuzzukanmu ta hanyar hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba. Koguna sun gurbata. Mun san cewa da zarar muna lalata dazuzzukanmu, yana matukar tasiri ga yanayinmu. Babu wani kuduri na kare muhalli daga gwamnati.
Ta bukaci gwamnati da ta dauki kwakkwaran mataki don tunkarar kalubalen muhalli a Ghana, ciki har da ayyana dokar ta-baci a dukkan yankunan da ake hakar ma'adinai.
Malam Jafar Dankwabia da yake mayar da martani ga jawabin shugaban, yace: ‘(shugaba Akufo-Addo) ya yi ikirarin cewa ya shuka bishiyoyi miliyan 50 … amma kuma bishiyoyin da ake yankawa domin hakar zinariya ba bisa ka’ida ba (ko galamsay) ya sa wadanda aka shuka ba za su yi mana amfani ba, saboda idan an shuka daya, aka yanke goma, to an koma baya’.
An fara taron kiyaye muhalli na COP, tun shekarar 1995 a kasar Jamus.
Taron na bana dai, ya maida hankali ne kan samar da kudaden gyara yanayi da taimakon kasashe masu tasowa don dakile illolin da sauyin yanayi ke haifarwa.
Saurari cikakken rahoton Idiris Abdallah:
Your browser doesn’t support HTML5