Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma Daraktan wasanni a kungiyar Ajax Marc Overmars, ya shawarci tsohuwar kungiyarsa ta Arsenal, da tayi kokarin maye gurbin dan wasanta Mesut Ozil, da dan wasan gaba na kungiyar Ajax, mai suna Hakim Ziyech.
Overmars, ya ce yayi matukar mamakin yadda har yanzu Arsenal ba ta nemi sayen dan wasan Ziyech ba, duk da cewa a bayyane take karara matashin dan wasan na Ajax yafi Mesut Ozil, idan aka duba a bangaren rarraba kwallo a cikin fili.
Dan wasan Ziyech, ya ci wa Ajax kwallaye 21, ya kuma taimaka wajen zura kwallaye 24 da kulob din taci a yayin kakar wasan da aka kammala ta 2018/19.
Rashin kokari da bajintar Ozil, a Arsenal ya samo asaline tun bayan da Umai Emery, ya karba ragamar jagorancinta, wanda hakan ya haifar da wasu muhawara kan makomar dan wasan a kakar wasa.
Marc Overmars, ya kara da cewar idan har kungiyar ta Arsenal tayi sa'ar dauko matashin dan wasan Ziyech, zai taimaka mata sosai a dukkanin wasanninta da take tunkara musamman na kakar wasa mai zuwa.