Akwai Bukatar a Taimaka Wa Masu Karamin Karfi - Hakimin Jimeta

A daidai lokacin da jama'a suka soma zama a gidajensu sakamakon matakan da ake dauka na yaki da yaduwar cutar coronavirus, sarakuna da wasu shugabannin al'umma sun yi kira da a tallafa wa masu karamin karfi.

A halin da ake ciki yanzu, bankuna da kuma kasuwanni sun dauki matakan dakile yaduwar cutar coronavirus, da suka hada da amfani da sinadarin wanke hannu a wuraren cire kudi da kuma shaguna, yayin da aka umarci ma'aikatan gwamnati su zauna a gidajensu sai yadda hali yayi.

Wasu mazauna jihohin Adamawa da Taraba sun ce matakin da gwamnatocin jihohin suka dauka na umurtar ma’aikata su zauna gidajensu yayi daidai, ko da yake wasu kuma na ganin hana mutane neman abinci ba abu bane mai yiwuwa.

To sai dai kuma yayin da talakawa ke bin umurnin gwamnati, wasu na ganin akwai bukatar gwamnati da masu hannu da shuni su tallafa musu.

Yanzu dai ‘yan jihohin Adamawa da Taraba sun zuba ido su ga irin taimakon da gwamnatocin jihohin suka ce zasu yi.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar a Taimaka Wa Masu Karamin Karfi - Hakimin Jimeta