Akwai Abin Dubawa Ga Matsalar Tattalin Arzikin Najeriya

Mata Da Suka Rasa Mazajensu A Sansanin Damare

Wasu mata da suka rasa mazajensu sun koka kan cewa yanzu haka suna cikin wani halin ban tausayi, sakamakon matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita, wanda don haka suka mika kokon bararsu da ake tunawa dasu.

Wata mace da mijinta ya rasu ya barta da ‘ya ‘ya Hudu, Madan Haske, tace yanzu rayuwa na yi musu wahala ita da ‘ya ‘yanta.

Ita ma kamar Madan Haske, wata yar gudun hijira daga garin Madagali, wadda ta rasa mijinta, tace yanzu haka ma tana gudun hijira ne a daki daya da wani ya taimaka mata ita da ‘ya ‘yanta guda Shida.

To sai dai kuma ganin irin halin da jama’a ke ciki yasa yanzu shugabanin addini yin kira ga jama’a da a dukufa da yin addu’o’i, domin karkato da hankulan mahukuntan kasar game da halin da talakawa ke ciki.

Sheikh Abdullahi Bala Lau, dake zama shugaban kungiyar Izala a Najeriya, ya bada shawarar cewa a hada da hakuri.

Amma ga masana irinsu Alhaji Muhammadu Haladu Dankwai Sardaunan Jimeta, na ganin akwai abin dubawa game da matsalar tattalin arziki da yan Najeriya ke kokawa akai.

Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Abin Dubawa Ga Matsalar Tattalin Arzikin Najeriya - 3'44"