Taron wanda shugaban kasar Amurka Joe Biden zai jagoranta, zai sabunta dangantakar Amurka da Afirka, da inganta hadin gwiwa kan muhimman batutuwan da suka shafi duniya baki daya.
Shugaba Akufo-Addo ya samu rakiyar uwargidansa, Rebecca Akufo-Addo; Ministar Harkokin Waje, Shirley Ayorkor Botchey; Ministan ciniki, Alan Kwadwo Kyerematen; Ministan Ayyuka da Gidaje, Francis Asenso Boakye; Ministan Muhalli, Kimiyya da fasaha da Ƙirkire-kirkire, Dokta Kwaku Afriyie; da wasu jami'ai a fadar shugaban kasa da ma'aikatar harkokin waje.
Masani a kan hulda tsakanin kasa da kasa da harkokin tsaro, Irbad Ibrahim, ya gayawa Muryar Amurka cewa wannan taro na da muhimmanci ga Amurka da kuma Afirka.
Ya ce, kasashen Rasha da China sun karfafa dangantaka da Afirka, domin haka ita ma ya kamata ta farfado da tsohuwar alakarta da Afirka. Haka kuma ya kara da cewa, Afirka ta bude sabon babi da za ta samu tallafi daga Amurka, kuma amfanin ya kasance ya tsaya a nan Afirka.
Mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum, Malam Isa Mairago Gibril Abbas ya ce lallai wannan taro zai bunkasa cinikayya da diflomasiya da dimokradiya ga Ghana da Afirka baki daya.
Kasar Amurka da wasu kasashen Afirka na da alaka mai karfi a bangarorin diflomasiya, tattalin arziki, tsaro da sauransu.
Yunus Salahudeen Wakpenjo, manazarci kan al’amuran yau da kullum ya ce, duk abinda ya gani na ci gaba a kasar Amurka, ya zo da su Ghana kuma ya kwatanta aikata hakan.
Shugaba Akufo-Addo zai dawo Ghana a ranar Asabar, 17 ga Disamba, 2022, kuma mataimakin shugaban kasa, Dr. Mahamudu Bawumia, zai yi aiki a madadinsa kamar yadda dokar kasa, sashe na 60 (8) ta tanadar.
Saurari rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5