Akon Na Shirin Kirkiro Wani Birnin Zamani a Senegal

Da alamar kasar Senegal za ta dada zama wata kasar zuwa yawon bude ido da harkokin kasuwanci ganin yadda Akon ke shirin gini wani birnin zamani a kasar.

Fitaccen mawakin nan na Amurka Akon y ace zai ci gaba da shirin da ya fara na kirkiro wani birnin zamani da zai ci dala biliyan 6, wanda zai rada wa sunansa a senegal

A ranar litinin Akon da jami’an gwamnati su ka tafi filin da za a gina birnin, wanda da ke garin Mbodienne, a kusa da Dakar babban birnin kasar Senegal.

Akon, wanda sunansa na asali shi ne Aliuane Thiam, ya ce yana ganin birnin nasa zai zamanto wani farkon ci gaban Afirka, sakamakon irin fasahohin da yake sa ran amfani da su kan birnin.

Akon wanda ya tashi a kasar Senegal tare da iyayensa, na sa ran birnin zai samar wa ‘yan Senegal ayyukan yi da dama.