Akwai Bukatar Inganta Fahimta Tsakanin Ma'aikatan Jiyya Da Masu Jiyya - Inji Magret Wilson Garba

Magret Willson Garba

Babbar matsalar da nake fuskanta a wajen aiki na kasancewar ina aikin jinya na jarirai shine rashin fahimta daga wajen iyaye ko masu jinyar yara mussamam ma ganin cewar aiki ne da ke bukatar kula inji wata malamar jinya matron Magret Wilson Garba

Ta ce da dama iyaye kan nuna rashin ganewarsu walau da gaske ko da gangan wanda yin haka kan kawo cikas ga yanayin aikin, wani lokacin har ta kai ma sai an kira wasu jami’an sun zo sunyi musu tsakani da iyaye.

Magret ta ce tun tasowarta take a matsayin diya mace take shi’awar aikin jiyya kuma Allah ya taimaka ta samu cimma burinta.

Daga karshe ta shawarci matasa musammam ma mata da su jajirce su nemi ilimi kasancewar canjin rayuwa da aka samu a yanzu , ko ba don aiki ba domin tarbiyantar da ‘ya'yan da zasu haifa idan kuwa karatun bai samu ba lallai sana’ar hannu ta zama wajibi ko don neman na kaiwa baki.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Fahimtar Juna Tsakanin Ma'aikatan Jiyya Da Masu Jiyya - Inji Magret Wilson Garba