Na fuskanci matsala da malamina a yayin da nake karatuna na Diploma inda ya nuna yana sona ni kuwa zuciya ta debe ni har ta kai ni da marinsa sakamakon na ki amincewa da abinda ya kawo mini inji wata matashiya malama Husna Wali.
Matashiyar ta kara da cewa wannan mataki da ta dauka ya ja mata matsala sosai domin kuwa a shekarar karshe sai aka kada ita a dukkanin jarabawar da ta rubuta aka kuma rubuta mata cewar babu takardar da ta zana sakamakon matakin da ta dauka akan malamin da ya nuna yana son ta, inji malama Husna.
Husna ta ce hakika mata na fuskantar matsaloli da dama mussaman a harka ta neman ilimi a mafi yawan lokuta ma su kan fuskanci matsaloli daga malamai kuma da zarar mace ta nuna bata son malami sai a kada da ita a makarantar ko a musguna mata har ta kai ta ga hakura da karatun da zarar ta ki amincewa da abinda wani malami ke bukata.
Husna ta ce sai da ta baro jihar Adamawa, wato asalin jihar ta zuwa jihar Kano sa’annan ta faro karatunta tun daga farko har ta kai a yanzu ta kamalla kuma a hannu guda tana sana'ar hannu wadda ta ke samu tana biyan bukatu da sauran hidimomin ta.
Daga karshe ta ja hankalin matasa maza da mata da su jajirce wajen neman ilimi tare da sana’ar hannu domin magance wa kai takaicin zaman duniya.
Your browser doesn’t support HTML5