An kashe akalla mutum bakwai kana wasu da yawa sun jikata a jiya Lahadi yayin da wani bom da aka sanya a mota ya tashi a arewacin Syria, a kusa da iyakar kasar da Turkiya, a cewar wani mai sa ido akan yaki.
"Wata mota dauke da bom ta fashe a wurin wani shataletale da ke zuwa har gaban kofar wurin binciken ketara iyakar Bab al-Salam," abinda Rami Abdel Rahman na kungiyar kare hakkin bil Adama ta Syrian Observatory, ya fada wa kamfanin dillancin labaran AFP kenan.
An kashe mutum bakwai, ciki har da farar hula biyar kana sama da wasu su sittin sun jikata, ciki har da mata da yara.
Yankin lardin da ke arewacin Aleppo, wanda ke karkashin ikon sojojin Turkiya da sojojin kawancen Syria, ya sha fuskantar munanan hare-hare da kuma kashe-kashe.
Kungiyar Observatory ta dora laifin harin na jiya Lahadi a kan kungiyar IS, ta na mai cewa ta yiwu maida martani akan karin hare-haren da dakarun Turkiya da wadanda ke goya musu baya ke yi kan wuraren 'yan IS a yankin ne.