Akalla Mutanen Rohingya 180 Ne Suka Rasa Rayukansu A Teku

Your browser doesn’t support HTML5

Mai yiwuwa, nutsewar da wani kwale-kwalen ‘yan gudun hijirar Rohingya ya yi dauke da mutum 180, ya zamanto hadari mafi muni da ya auku a teku a ‘yan shekarun bayan nan. Lamarin ya auku ne yayin da ‘yan gudun hijirar na Rohingya, wadanda Musulmai ne, ke tserewa matsananincin halin a Bangaladesh.