Akalla mutane 73 suka rasa rayukkansu, wasu fiyeda 100 suka ji raunukka iri-iri lokacin da wata motar daukan man fetur ta yi bindiga, mutane suka zo suna kokarin dibar man da ya zube daga cikinta a kasar Mozambique.
WASHINGTON DC —
Wadanda suka shedi hatsarin sunce motar ta fadi, ta juye ne a wani kauye dake lardin Tete, can kusa da inda Mozambique tayi kan iyaka da kasar Malawi.
Rahottanin farko da aka soma samu sunce zafin rana da ya zafafa motar ne ya sa ta kama da wuta. Mozambique, wacce tana daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, har yanzu bata farfado ba daga yakin basasar da tayi fama da shi, wanda aka karkare a shekarar 1992.
Haka kuma kasar, wacce ke a sashen kudu-maso-gabashin Afrika, tana fama da Fari da kuma masifar karancin abinci.