Akalla Mutane 15 Suka Rasa Rayukansu A Somalia

Mutanen dake gudu daga harin da al-Shabab ta kai kauyukansu

Harin da al-Shabab ta kai tsakiyar kasar Somalia a kokarin diban kananan yara a wani kauye domin horas dasu su zama mayakansu ya yi sanadin mutuwar mutane 15

Akalla mutum15 ne suka rasa rayukansu a yankin tsakiyar kasar Somalia, bayan wata arangama da ta auku a tsakanin wasu mazauna karkara da mayakan Al Shabab, wadanda suka yi yunkurin diban kananan yara a wani kauye a matsayin wadanda za su mayar mayakansu.

A cewar majiyoyin cikin gida, mayakan Al Shabab 10 ne suka mutu kana mazauna karkara biyar suka riga mu gidan gaskiya a kauyen Aad da ke tsakiyar hukumar Galmudug.

Wani mazaunin kauyen da ya nemi da kada a bayyana sunansa, ya fadawa Sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, kwanaki biyu da suka gabata, mayakan na Al Shabab, sun tattauna da wasu shugabannin kauyen guda biyu, inda suka nemi da ba su mayaka.

“Fadan ya kaure ne bayan da suka nemi a mika musu kananan yara a matsayin mayaka,” mazaunin kauyenm ya kara jaddawa.

Ya kara da cewa, daga haka ne kuma, sai mazauna kauyen suka hada kansu suka nuna tirjiya ga mayakan Al Shabab, amma daga baya sai ‘yan kungiyar ta Al Shababa suka karbe ikon kauyen.