Mutane akalla 10 suka rasa rayukkansu yau a Afghanistan a sanadin tashin wasu fashe-fashe har guda ukku na bama-bammai da suka faru a wajen da ake gudanarda jana’izar wani matashi dan wani dan majalisar dattawa na kasar da aka kashe jiya Jumu’a a cikin gagarumar zanga-zangar da aka gudanar a Kabul, babban birnin kasar.
A wajen jana’izar yaron da akace dan Senator Alam Ezadyar ne, akwai tarin manyan mutane da suka hada jigogin majalisar dokoki da kuma babban kantoma Abdullah Abdullah.
An kai wannan harin ne a daidai lokacinda ake ci gaba da aiwatarda dokar ta-baci akan a birnin na Kabul a sanadin da wancan zanga-zangar ta jiya wacce aka ci gaba da yinta har zuwa yau Assabar.
Mutane akalla hudu aka kashe a jiya cikin rigimar inda mutanen da suka taru suna neman sai a karfafa matakan tsaro, suka gwabza da ‘yansanda.
Mutanen na Afghanistan dai sun fusata ne da mummunan farmakin da aka kai a can Kabul ranar Larabar da ta wuce, inda aka hallaka mutane 90, aka raunana wasu 450.
Wannan farmakin da aka kawo yayinda ake cikin azumin watan Ramadan, yana daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka ga an kai a Afghanistan tun 2001.