Wasu majiyoyi kuma sun bayar da adadin da ya fi haka, inda suka ce an kashe mutane 17 ciki har da yara.
Mace macen na garin Bauchi na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da tabarbarewar tattalin arziki mafi muni a kasar, kuma a yayin da yan kwanaki kadan bayan da dalibai biyu suka mutu a wani taron kyautar da buhunan shinkafa a garin Keffi da ke yankin tsakiyar kasar.
Da sanyin safiya, mata da kananan yara suka taru a kofar ofishin wani hamshakin attajiri a cikin garin Bauchi, inda suka karbi kyautar kudi naira 5,000 ($3.40) domin biyan kudin abinci a watan Ramadan.
Shaidu sun ce jama’a sun yi ta turereniya don su amshi kudaden, lamarin da ya haifar da turmutsitsin.
“Mun samu rahoto daga Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa cewa an kawo mata biyar asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon turmutsitsi da aka samu a yayin rabon kudi da mai kamfanin Shafa Holdings ya yi.” Inji kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi Mohammed Wakil.
“An tabbatar da mutuwar hudu daga cikin matan yayin da ta biyar ke ci gaba da jinya a asibiti,” inji Wakil, inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike.
Wani ma’aikacin Shafa Holdings, Shafiu Umar ya ce mutane 17 ne suka mutu a turmutsitsin da suka hada da yara 10 da mata bakwai.
“Mutane sun fi yadda ake tsammani kuma wadanda suka ci gajiyar tallafin sun yi ta ture-ture da ake bayar da tallafin, wanda ya haifar da mummunan turmutsitsi,” in ji Umar.
Wani jami’in hukumar tsaro da ke wurin shi ma ya shaida cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 17.
“Yawancin mata sun zo daga nesa da kusa, wasu tare da ‘ya’yansu,” in ji jami’in da ya nemi a sakaya sunansa.
Najeriya dai na ta fama da tashin gwauron zabin kayan abinci tun bayan da gwamnati ta janye tallafin man fetur tare da canja karfin Naira a wani yunkuri na bunkasa tattalin arzikin kasar.
Hauhawar farashin kayayyaki ya kai na mizanin sama da shekaru 30 wato kashi 31 da digo 7 cikin ɗari, wanda hakan ya sa mutane da yawa ba su iya sayen kayayyakin yau da kullum.
Galibin ‘yan Najeriya na rayuwa ne a kasa da dala 2 a rana kuma da yawa sun daina cin abinci sau uku a rana tare da hakura da kayan abinci irinsu nama da kwai da madara.
A farkon watan nan ne hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta ce an tsaurara matakan tsaro a ma'ajiyar abincinta bayan da wasu daruruwan mutane suka wawushe wani kantin sayar da abinci a Abuja babban birnin kasar.