Rundunar sojojin Najeriya ta zargi mutanen ukku da take nema da cewa suna da masaniya akan inda kungiyar Boko Haram take tsare da 'yan matan Chibok da ta sace.
Shi dai dan jarida Ahmed Salkida ya kakabawa kansa gudun hijiran dole a Dubai. Ahmed Bolori tuni ya ziyarci sojoji jiya a Maiduguri amma suka ce ya dakata. Sai kuma Barrister Aisha Wakil wadda ita ma ta mika kanrta wa sojoji a Birnin Abuja.
Muryar Amurka ta kirata ta wayar hannu kuma ta tabbatar tana Abuja a hedkwatar sojojin Najeriya. Tace da ta bayyana kanta a ofishin wadda ke karban mutanen dake shiga hedkwatar tace mata bata da masaniya a kanta. Aisha tace ta kawo kanta ne domin an ce ana nemanta ruwa a jallo.
Bayan ta rubuta sunanta sai wani soja ya fito ya dauki hotonta kana yace ta jira.
Aisha Wakil tace sojojin sun santa sosai. Idan kuma akwai abun da suke bukata me ya sa basu zo gidanta ba domin sun san gidan. Tace suna zuwa gidanta duk lokacin da zata gana da babban hafsan sojojin Najeriya, su dauketa. Suna kuma da lambar wayarta.
Tace bayyanata a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo wulakanci ne.
Wani masanin shari'a Yakubu Malumfashi lauya mai rajin kare hakkin bil Adam yace kafin a ce ana neman wani ruwa a jallo dole sai an tabbatar ya aikata wani mugun laifi.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5