Uwargidan gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce sam ba ta ba da umurnin a damke dogarin ta Sani Baban Inna ba, bisa zargin zambatar mutane ko amfani da sunan ta wajen amsar na goro daga wajen masu son alfarma.
A sanarwa daga fadar shugaban Najeriya da Jaridar Daily Trust ta wallafa, Aisha Buhari ta ce ba ta taba aikan wani ya karbo ma ta wani kudi ba don haka ta ke bukatar wadanda ke kan madafun iko su wuce samun damuwa daga wata tsoratarwa daga hadiman su, da nuna sam ba za ta lamunci ha’inci daga duk wani mai aiki da ita ba.Hakanan ta bukaci duk wadanda ke zargin Baban Inna ya karbi kudi a wajen su, da su je su nemi kudin su a wajen sa.
Rahotanni da mu ka samu tun farko sun baiyana cewa rundunar ‘yan sanda ta yi awon gaba da dogarin jami’in ‘yan sanda Sani Baban Inna dan gudanar da bincike bisa zargin ya ki mika kudi Naira biliyan 2.6 da wasu su ka yi yunkurin turawa uwargidan shugaban don samun alfarma.
Kafin kama shi Baban Inna ya shaidawa abokan aikin sa cewa sam bai karbi ko sisin kwabo da sunan uwargidan shugaban ba ballanatana har a kala ma sa zargin ya gina gida na Naira miliyan 200.
Baban Inna daga jihar Adamawa, jihar su uwar gidan shugaban, ya fara aiki da Hajiya Aisha a matsayin dogari tun shekarar 2016.