Aisha Buhari Ta Kaddamar da Shirin Duba Lafiyar Mata a Yola

Aisha Buhari, matar shugaban kasa Muhammad Buhari

Matar shugaban Njaeriya Hajiya Aisha Buhari ta kaddamar da shirin duba lafiyar mata a garin da aka haifeta inda kuma ta yi karatun firamare, wato Yola jihar Adamawa

Matar shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta kaddamar da shirin duba lafiyar mata saboda gano cututuka irin cutar sankarau ta mahaifa dakuma ta nono.

Irin wadannan cututukan sukan yi yawa a kasashe masu tasowa kamar Najeriya.

Yayinda take kaddamar da shirin a garin Yola wanda ya kasance mahaifanta inda kuma ta yi makarantar firamare ta bukaci gwamnonin jihohi da shugabannin kananan hukumomi da su bi sahu saboda a samu nasara wajen bunkasa kiwon lafiyar mata.

Hajiya Buhari ta yabawa likitocin da suka sadakar da kansu saboda taimakawa shirin nata.

Tace ta fara shirin ne a garin Calabar kodayake bata samu ta kasance wurin ba. Amma ta samu zuwan na Yola wanda kuma garinta ne. Ta godewa mutanen da suka fito tare da likitoci da suka bada gudummawa. Tace babu wanda aka biya kama daga nus zuwa likitocin.

Kimanin mata dubu biyu ne daga kananan hukumomin jihar 21 aka duba lafiyarsu. An dubasu kan cutar sankarau da ciwon sikari da hawan jini da idanu da ma hakora.

Wasu matan ma 'ya'yansu suka kawo. Duk magungunan da aka raba kyauta ne. Babu wadda ta biya ko kwandala.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Aisha Buhari Ta Kaddamar da Shirin Duba Lafiyar Mata a Yola