Aikin Kwashe Mutane daga Aleppo Ba Zai Wuce Kwana Biyu Ba

Taron ministocin harkokin wajen Rasha da Turkiya da Iran akan kwashe mutane daga Aleppo kasar Syria

Ministocin harkokin wajen Rasha da Turkiya sun fada a jiya Talata cewa aikin kwashe mutane daga birnin Aleppo da kewaye ba zai dauki sama da kwanaki biyu ba.

Izuwa yanzu an kwashe mutane sama da dubu 37 daga birnin, kuma babban burin da aka sa a gaba shine a ga an kwashe dukkan sauran mutanen da suka rage a garin na Aleppo kafin karshen yinin yau Laraba, acewar ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu, a wani sakon da ya dora a kan shafinsa na Twitter a jiya Talata

A karshen wani taron da aka yi tsakanin ministacin harkokin wajen Rasha, da Turkiya da kuma Iran a birnin Moscow ne, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya shaidawa yan jarida cewar kasashen uku sun yi amfani da tasirinsu wurin yin matsin lamba don a hanzarta kamalla aikin kwashe mutanen dake Aleppo, inda ya kara da cewa yanzu kasashen nasu sun zama masu ruwa da tsaki a yakin Syria na tsawon shekaru shida

Ministocin kasashen wajen sun shata wasu shawarwari da Rasha tace ana iya anfani da su wajen tsagaita har ma da kawo karshen wannan yakin baki dayansa.

Rasha ta kara kaimi wurin daukar wannan matakan ne sakamakon kissan gillar da aka yi wa jakadanta a Turkiya.